Majalisar Malaman Afrika

Bismillshir- Rahmanir- Rahim

1.0 Gabatarwa:

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da aminci su tabbata ga wanda Allah ya aiko a matsayin rahama ga talikai, da alayensa da sahabbansa da waxanda suka bi sawunsu da kyautatawa, har zuwa ranar sakamako.

 

1.1 Shimfixa:

Tunanin kafa wannan Majalisa ta malaman Afrika, wadda take kudancin sahara, ya daxe ana tawan sa a duk lokacin da aka haxu a wuraren taruka da sauran hidimomi, irin waxanda malaman Afrika kan halarta tare da bayar da tasu gudunmawa. Sawa’un waxannan taruka, irin waxanda ake shiryawa ne tare da gudanarwa a cikin wannan yanki na Afrika ko a wajensa. Kai har aka wayi gari wannan tunani ya zama wani abin tattaunawa da tsokaci a tsakanin malaman wannan nahiya, ta hanyar musayar saqonni irin na kar-ta-kwana ta hanyar kafafen sadarwa na zamani. A haka har aka gamsu da cewa, lokaci fa ya yi, wanda ya kamata a cikinsa, a fito da wannan tunani a fili kuma a aikace. Musamman, saboda ganin irin yadda sabbin abubuwa da dama, suke ta karakainar faruwa kuma a cikin gaggawa a duniyarmu ta yau,  mai cike da qungiyoyi da majalisu barkatai, farare da baqaqe.

Abin da yake tafe a cikin wannan takarda, wani xan taqaitaccen tarihi ne na wannan Majalisa, da irin yadda aka shimfixa tare da kafa ta tun farko har zuwa yau.

1.2 Manufa:

An yi tunanin kafa wannan Majalisa ne a kan tunani, da manufar ta zama wani qasaitaccen zaure ga malaman wannan yanki na duniyar Afirka da ke kudancin sahara, wanda zai zama wata makoma ta ilimi da neman fatawa, tare da yin gagarumin tasiri a tsakanin gaba xayan al’umomin Afrika. Wata manufar kuma ita ce, inganta matsayi da irin gudunmawar da malamai da masu wa’azi suke bayarwa, a wayi gari sun zama jagoran rayuwa  ga gaba xayan al’umomi da qabilu da suke rayuwa wannan yanki, ta hanyar samarwa fatawa cikakken tsari da kangado. Gurin wannan Majalisa ne, ta  riqa tsoma baki a cikin al’amurra da matsalolin rayuwar jama’ar wannan yanki, ta gaba xaya. Sa’annan kuma ta zama ita ce ke magana da yawun bakin musulmin wannan yanki na Afrika a xaukacin tarukan cikin gida, da na waje, da ma na matakin duniya baki xaya.

 

1.3 Quduri:

Babban qudurin wannan Majalisa shi ne, samar da wata makoma ta ilimi irin na Shari’ar Musulunci, wanda zai zama sanadi kuma ginshiqin xaukaka da cigaba da bunqasar al’ummar musulmi da suke cikin wannan yanki na Afrika.

1.4 Nauyi:

Babban nauyin da yake kan wannan Majalisa shi ne rayawa, ingantawa tare da fitowa da qoqarce-qoqarcen malaman nahiyar Afrika, da haxa kansu a matsayin tsintsiya maxaurinki xaya, domin hakan ta ba su cikakkar damar jagorancin al’umominsu a bisa ingantaccen tafarki na Musulunci.

1.5 Dalilan Kafa Majalisar:

Akwai manyan dalilai, da suka haifar da tunanin kafa wannan majalisa, da suka haxa da

1- Rashin wani zaure qwara xaya, da ake da shi a wannan nahiya, a matsayin makoma da musulmin Afrika a cikin al’amurra na ilimi.

2- Rashin sauti xaya, da yake wakiltar gaba xayan musulmin wannan nahiya idan ana zancen manyan matsaloli, da suka shafe su a matsayin al’umma.

3- Yawaitar matsaloli da tashe-tashen hankula, da sauran nau’ukan gwagwarmayoyin rayuwa, waxanda musulmi suke cikinsu tsundum.

4- Warwatsewar qoqarce-qoqarcen malaman da’awa, da rashin haxin kan da yake tsakaninsu.

5- Rashin isasshen ilimi da zai bayar da damar bayar da ingantattun fatawoy

 

 1.6 Manyan Dokokin Gudanarwa:

Manyan dokokin gudanar da wannan Majalisa a matsayin siyasar tafiyarwa, sun haxa da:

 1. Aiki da Alqur’ani da Sunna bisa fahimtar magabatan farko shiryayyu, bisa aqida matsakaiciya, wadda babu zurfafawa ko kasawa a cikin ta.
 2. Kula da gaba xayan yankunan wannan nahiya ta Afirka komai nisan su, ta vangaren kafawa da gudanarwa, tare da samar da wakilci na haqiqa daga kowane yanki na nahiyar.
 3. Gudanar da ayyukan Majalisa bisa tsari na cin cikakken gashin kai, tare da nisantar karvar umarni daga kowace irin qasa ko qungiya.
 4. Qulla kyakkyawan zumunci da gaba xayan al’umomin nahiyar Afirka, ta hanyar alkinta matsayin wakilansu, tare da shirya taruka a qasashe da garuruwansu, waxanda suke xauke da saqo mai ma’ana da manufa da kamanni iri xaya.
 5. Amfani da qwararru a fagen ilimi da aiki, domin xaukar matakai da yanke shawarwari, da bayyana fahimta da ra’ayoyi.
 6. Dogara a kan hanyoyi da dabaru irin na hikima da fasaha a fagen ilimi, domin mu’amala da wasu qungiyoyi masu zaman kansu, da ma’aikatun Gwamnati, da sauran vangaroran al’umma, waxanda ba fahimtarmu xaya ba, da su.
 7. Yin cikakken amfani da hanyoyin sadarwa da kafofinta, na zamani a fagen yaxawa da isar da saqonnin Majalisar a faxin nahiyar Afrika.
 8. Majalisar kuma, za ta buxe qofofinta ga maza da mata, da suke son yin aiki tare da ita, amma, bisa sharuxxa da qa’idoji irin na Shari’ah.

1.7 Gurace-gurace:

Gurace-guracen wannan Majalisa sun haxa da:

l. Samar da wata makoma ta ilimi da da’awa, wadda za ta riga daidaitawa da kuma tsara yadda ya kamata qoqarce-qoqarcen malamai, na ilimi da da’awa, su gudana a wannan nahiya ta Afrika.

ll. Samar da qasaitacciyar makoma ta Musulunci, wadda za ta riqa magana da yawun musulmin nahiyar Afrika, a duk lokacin da aka haxu da qungiyoyi da ma’aikatu na ilimi da jami’an gwamnatocin qasashe da kuma na qasa da qasa.

lll. Bayar da gudunmawa tare da raya qoqarce-qoqarcen da malamai suke yi na karantarwa da ilmantarwa ga al’umomin wannan nahiya ta Afrika.

lV. Karve kakakin fatawa daga hannun waxanda ba su cancanta ba, musamman a cikin manyan al’amurra da suka shafi gaba xayan al’ummar nahiyar Afrika.

V. Samarwa tare da inganta zaman lafiya tsakanin manya da qananan al’umomin nahiyar Afrika.

Vl. Samarwa tare da buxa kafafen sadarwa domin hulxa da wasu Majalisu da qungiyoyi na Musulunci masu irin wannan hidima da kula da al’amurran al’ummar musulmi.

 1.8Hanyoyi:

Domin tabbatar da cin nasarar gudanar da waxannan gurace-gurace, wannan Majalisa za ta bi hanyoyi kamar haka:

 1. Shirya yadda al’amurran ilimi da da’awa da tarbiyya za su riqa gudana a wannan nahiya ta Afrika.

 1. Kafa wuraren gudanar da hidimomi irin na ilimi da da’awa da tarbiyya, da kuma kula da su.

 1. Bunqasawa da qarfafa qungiyoyi da cibiyoyin harkokin Musulunci na cikin gida da qananan yankuna.

 1. Bugawa tare da watsa bayanai a kan manyan al’amurran da suka shafi al’umma, ta hanyar kafafen sadarwa.

 1. Gabatar da nasihohi da gargaxi da luraswa ga dukan vangarorin da suke bukata.

 1. Yin tsaye tsayin daka a kan ganin an warware rikittan da suka shafi musulmin wannan nahiya.

 1. Bayar da fatawa a kan manyan al’amurra da sabbin matsaloli.

 2. Raya Masallatai da mimbarorinsu, da kuma samar musu da limamai da malamai waxanda suka cancanta, domin saqon da suke isarwa ga al’umma ya zama nagartacce.

 1. Shirya taruka manya da qanana irin na ilimi da da’awa, tare da shirya taruka irin na qara wa juna ilimi da za su shafi gaba xayan nahiyar.

 1. Shirya waxansu taruka irin na koyarwa da havaka hikima da fasaha, don amfanin ‘ya’yan wannan nahiya masu baiwa ta musamman.

 1. Samar da tsararrun bayanai da suke magana a kan Musulunci, a wannan nahiya ta Afrika, waxanda za su bayar da cikakkar damar nazarin Musulunci da sanin makamarsa a cikin sauqi da sauqaqewa.

 1. Shiryawa tare da bugawa da yaxa ayyukan bincike da nazari.

 1. Samar da waxansu shiraruwa waxanda za a riqa saurare da kallo, a cikin harshen Gwamnatotan qasashe da qabilun Afrika.

 1. Samarwa tare da amfani da gaba xayan kafofin sadarwa.

1.9 Qa’idojin Zaven Mambobi:

Qa’ida ne kafin a zavi mutum a matsayin manba a wannan Majalisi, ya cika waxannan sifofi:

– Lallai ne ya kasance mutum mai cikakken tasiri da faxa a ji a yankinsa.

– Lalle ne ya kasance mai kyakkyawan tarihi; ba wanda ya shahara da ayyukan varna da baxala ba.

1.10Tsare-tsaren Bunqasa Ayyukan Mambobi:

Saboda bukatar da take akwai ta bunqasawa tare da inganta ayyukan mambobin wannan Majalisa a tsakanin jama’arsu, wannan Majalisa ta xauri aniyar gudanar da waxansu tsare-tsare, da gabatar da waxansu hidimomi zuwa gare su. Amma, da sharaxin rashin kasancewar waxannan abubuwa samammi gare su qarqashin tanade-tanaden da suke hannun cibiyoyi da sauran qungiyoyi abokan aiki, da suke kula da irin wannan hidima ta da’awa da sauran ayyukan Musulunci, a yankunasu. Waxannan tsare-tsare sun haxa da:

 A. Samar da adiresai da sauran shafukan ilimi a yanar gizo, da za su sauqaqe hanyar watsawa da yaxa karance-karance da fatawowinsu.

 B. Alkinta yanayin Masallatai, da gina cibiyoyi, da samar da xakunan karatu.

C. Tabbatar da ganin an naxa an kuma watsa aikace-aikacensu na ilimi da da’awa, tare da kusantar da su ga al’umma da sauran xaliban ilimi.

D. Shirya taruka irin na bayar da horo domin bunqasa yanayin jagoranci da tasiri da qwarewar da suke da su.

1.11 Tsarin Shugabanci:

A) Manyan Ginshiqai:

 • Al-Jam’iyyatul Ámmah (Mahaxar dukan mambobi)

 • Al-Mu’utamarul Ám (Taron wakilai na ko ina)

 • Al-Majalisul Ám (Babbar mahaxar shugabanni)

B) Majalisar Zartaswa:

 • Arri’ásah (Shugabancin Majalisa)

 • Al’amanatul Ámmah (Sakatariya)

 • Al-Lijánul Fanniyyah wal- Far’iyyah Addá’imah (Kwamitoci na ayyuka na musamman da kuma na din-din-din)

 1.12 Qa’idojin Zaven Babban Ofishi:

Kafin a zavi wuri a matsayin inda za a kafa babban ofishin wannan majalisa, sai an yi la’akari da waxannan abubuwa kamar haka:

 • Rinjayen Musulunci a wurin.

 • Rinjayen Sunnah a wurin.

 • Rashin tashe-tashen hankali irin na Siyasa.

 • Sassafcin dokokin rajista da ayyukan qungiyoyi.

 • Qaqqarfan asasi irin na a zo a gani a fagen na’urorin sadarwa.

 • Wadatar rukunnai da muqarraban gudanar da ayyukan Musulunci.

1.13 Matakan Kafa Majalisar:

 • Mataki na Farko: Tunani

Tunanin samar da qasaitacciyar makoma ta Musulunci a farfajiyar nahiyar Afrika, tunani ne da ya samu gindin zama a zukatan malamai da sauran masu ruwa da tsaki a cikin ayyukan Musulunci a cikinta. Sauran abin da ya rage kuma na wannan tunani, ya cigaba da bunqasa ne ta hanyar tattaunawa a tsakanin waxannan rukuna biyu, a duk inda suka haxu a wasu taruka, da kuma ta hanyar kafafen sadarwa na zamani a matakin xaixaiku. A haka har aka cimma mataki da qoqarin aiwatarwa. Sai dai akwai bukatar samar da wani rukuni da zai kula da tuntuva da bibiya, da kuma tanade-tanade na wajibi.

 • Mataki na Biyu: Kafawa

Bayan gudanar da shawarwari da musayar tunani da nazari, sai aka cimma matsayin cirata daga wannan mataki zuwa mataki na gaba, wato kafawa. Waxanda kuma aka tuntuva a lokacin gudanar da waxannan shawarwari sun haxa da:

– Dr. Muhammad Ahmad Lauhu, daga Senegal

– Dr. Sa’id Muhammad Baba Sílah, daga Málí

– Dr. Muhammad Sani Umar, daga Najeriya

Bayan haka ne fa, aka samu kammala samar da asasin wannan Majalisa a cikin qwaqwalwa, a kan hanyar ciratar da shi zuwa haqiqa. Waxannan bayanai ma da muke gabatarwa yanzu suna daga cikin waxancan tsare-tsare.

 • Mataki na Uku: Bayar da Sanarwa

Wannan shi ne babban mataki kuma ginshiqi a fagen qoqarin kafa wannan Majalisa. A wancan mataki na kafawa, mambobinsa sun riga sun samar da asasi na farko, wanda a cikinsa aka amince da zavar waxansu zaqaquran malamai na wannan nahiya ta Afrika, waxanda za su zama su ne mambobin kwamitin tabbatarwa da kafa Majalisar, da suka haxa da:

– Dr. Muhammad Ahmad Lauhu, daga Senegal

– Dr. Sa’id Muhammad Baba Sílah, daga Málí

– Dr. Muhammad Sani Umar, daga Najeriya

– Dr. Bashir Adam, daga Ghana

– Dr. Sa’id Burhan, daga Juzrul- qamar

– Dr. Musa Fadiga, daga Sahilul- Áj

– Dr. Yahaya Abdallah Ahmad, daga Chadi

– Shaikh Khalfan Khumais, daga Kenya

– Shaikh Gahutu Abdalkarim, daga Ruwanda

– Shaikh Muhammad Zainu Zahruddin, daga Ethopia

– Shaikh Salim Bar Hayyan, daga Tanzaniya

– Shaikh Bilal Isma’il, daga Afrika ta kudu

Ba tare da wani vata lokaci ba, sai wannan kwamiti ya shiga aikinsa gadan-gadan, ta hanyar amfani da kafafen sadarwa na yanar gizo da sauran shafukan sadarwa na zamani, da tattaunawa ta hanyar waya. A qarshe, aka yanke shawarar haxuwa a birnin Makka mai alfarma, a daidai lokacin gudanar da aikin Umra, domin gudanar da tattaunawa ta qarshe a kan yadda wannan Majalisa za ta kasance, da kuma bayar da sanarwa a kan ta, daga wannan bigire, inda hasken Musulunci ya samo asali. Wannan haxuwa kuwa ta kasance ne tsakanin 7-12 ga watan rabi’us sání 1432H wanda ya yi daidai da 9-14 ga watan Maris 2011, wanda takwas daga cikin mambobin wannan kwamiti suka samu halarta. A qarshen wannan haxuwa kuma an yi matsaya a kan waxannan abubuwa:

 

 1-  Tabbatarwa tare da shimfixa tsarin asasin wannan Majalisa.

2- Shirya tsare-tsaren gudanar da babban taron qaddamarwa, da ambata inda za a yi. A qarshe, aka amince da gabatar da taron a Bamako babban birnin qasar Mali, a tsakanin 7 zuwa 9 ga watan Rajab 1432, wanda ya yi daidai da 8 zuwa 10 ga watan 7 na Daga baya kuma aka aminta da xaga shi zuwa 9 zuwa 11 ga SSha’aban 1432, wanda ya yi daidai da 8 zuwa 10 ga Yuli 2011.

3- Zave tare da samar da jerin sunayen waxanda za su zama mambobin farko, zakarun gwajin dafi, gwargwadon masaniyar da su ‘ya’yan wannan kwamiti suke da ita a kan kowane xaya daga cikinsu. Sa’annan kuma a bar qofar zauren a buxe domin bayar da damar cigaba da zaqulo irin waxannan mutane, da suka cika sharuxxan da aka gindaya tun da Babbar matsalar da aka fuskanta a wannan mataki, ita ce samun cikakken adireshin mutanen da aka ga dacewarsu, balle a iya sanar da su. Sai dai kawai aka sha alwashi tare da lasar takobin tabbatar da ganin an isar musu da wannan saqo ta kowane hali, bayan wannan taro, domin su samu damar halartar taro na gaba wanda shi ne mafi muhimmanci, sai kuwa wanda samun adireshin nasa ya faskara.

4- Samar da wata cibiya, wadda za ta yi riqon qwarya na jagorancin wannan Majalisa, wadda kuma ita ce za ta tsara yadda wannan babban taro na qaddamarwa zai kasance.

5- Zana taswirar tsare-tsaren da suka zama dole don shiryawa da gudanar da wannan taro na qaddamarwa. 

6- Samar da jadawalin tabbatar da gurin wannan Majalisa na shekaru hamsin nan gaba.

7- Tuntuvar manyan qungiyoyin bayar da agajin ayyukan alhairi, na Afrika domin nemo gudunmawar gudanar da wannan taro.

 

1.14 Babban Taro:

Allah, cikin ikonsa an samu gudanar da wannan babban taro na qaddamar da wannan Majalisa kamar yadda aka tsara; a garin  Bamako, babban birnin qasar Mali, wanda baqi da daman gaske daga wannan nahiya ta Afrika da wajenta suka halarta. Daga wannan lokaci ne kuma aka bayar da sanarwar kafuwar wannan Majalisa ta Malaman Afrika. Lokaci wanda, daga bayansa ne kuma aka shiga aiki gadan-gadan, a matakin ginawa, da aiki irin na haxin guiwa.

1.15 Abokan Aiki:

Tun lokacin da wannan Majalisa ta karvi zanannen sunanta, take neman abokan aiki irin ta, waxanda suka damu da al’amurran Musulunci a faxin wannan nahiya ta Afrika, domin ta haxa hannu da su. Ta kuma yi haka ne sakamakon nazarin qwaqwaf tare da shata vangaroran da ake da bukata da wannan qawance a cikin su. Wannan qawance kuma, abu ne mai sauqi, ya wuce iyakokin wannan nahiya ta Afrika, ya haxa har da waxansu vangarora na musayar dabaru, da sha’anin kuxi, da qwarewa, da tsare-tsare a wasu vangarora da al’amurra daban-daban.

1.16 Kammalawa:

Mafi girman abin da ya kamata mu kalla a daidai wannan mataki, shi ne abin da Allah Maxaukakin Sarki ya gaya wa Annabinsa sallallahu alaihi wa sallam, wanda shi ne jagora kuma babbar Makarantarmu, wato: “Kuma ka yi shawara da su a cikin al’amari. Kuma idan ka yi azama, to, ka dogara ga Allah. Lalle ne Allah yana son masu tawakkali.”  Suratu Ali Imran: 159

 

 Alhamdu lillah