Babban Taron Hadaddiyar Kungiyar Malamai ta Afrika, Karo na Biyu:
A cikin iyawar Allah, a wannan shekara Hadaddiyar Kungiyar Malaman Afrika ta gabatar da taronta na biyu a wuri mafi tsarki, kuma a lokaci mafi daraja.
Taron wanda aka tsara gudanar da shi duk shekaru biyar ya kasance a bana ne a cikin birnin Makka mai alfarma, kuma a cikin watan Dhul Hajji Mai tarin alfarma da albarka da daraja. Kimanin mahalarta 205 ne daga sassan Afrika suka halarci wannan taron, akasarinsu limamai ne da shugabannin al’umma masu karantarwa a Jami’oi da kuma masu kira da kuma karantar da addinin Musulunci daga kasashe 46 na Nahuatl Afrika ta kudancin Sahara. Taron ya gudana a tsakanin 3-4 ga watan Dhul Hajji 1439H (14-15 ga Agusta 2018). Da yawan mahalartan sun zo ne a cikin ayarin bakin da Mai Alfarma Sarki Salman ya gayyata a karkashin kulawar “Kwamitin Da’awa na Afrika”. Wasu kuma sun zo ne a matsayin jami’ai a hukumomin Alhazai na kasashensu.
An yi zama guda bakwai a cikin Taron:
Zama Na Farko: Budewa, in da Shugaban Kungiyar Farfesa Sa’id Burhan Abdallah ya gabatar da jawabinsa. Sai kuma bayanin yadda aka tsara taron daga Sakatare Janar Dr. Sa’id Muhammad Baba Sila. Sai kuma jawabin Mai masaukin baki, wanda Ustaz Usman Al-Usman Sakatare Janar na kwamitin Da’awa na Afrika ya gabatar a madadinsa.
A zama na biyu an gabatar da ayyukan kungiya da kuma bayanin abinda ya shafi shiga da ficen kudade a asusun wannan kungiya.
An kebance zama na uku zuwa na biyar ga ayyukan kwamitoci daban daban da aka kafa wadanda suka hada da, kwamitin tabbatar da tsarin gudanarwa da na shirya jadawalin ayyukan shekaru biyar, da kuma kwamitin tantancewa da karbar sababbin membobi.
A zama na shida, an tattauna rahotannin wadancan kwamitocin da shawarwarin da suka gabatar wadanda suka hada da canja wasu sassa na tsarin gudanarwa da wasu ayyukan da ya kamata ayi a shekaru biyar masu zuwa, da kuma sunayen wasu Malamai da ya kamata a shigo da su. An kuma samu cimma matsaya a kan duk wadannan abubuwa.
Zama na Bakwai: Rufe taro. Wannan zaman ya samu halartar jama’a masu dinbin yawa. A nan ne kuma aka karanta jawabin bayan taro, sai kuma jawabin sabon shugaban da aka zaba don jagorantar zango na biyu, sannan jawabin Mai masaukin taro, Mai martaba Dr. Bandar Bn Salman Bn Muhammad Al-Sa’ud. Sai kuma jawabin Shugaban taro, Farfesa Muhammad Ahmad Lauh. Sannan jawabin bako na musamman, Shugaban gudanarwa na Masallatai biyu masu alfarma na Makka da Madina; Sheikh Dr. Abdurrahman bn Abdallah Al-Sudais, wanda kuma shi ya rufe taron da karatun Alkur’ani.
A cikin taron dai an sabunta zaben Shugaban kwamiti Farfesa Sa’id Burhan Muhammad da Shugaban kwamitin amintattu Dr. Ahmad Muhammad Lauh da kuma Sakatare Janar Dr. Muhammad Baba Sila da mafi yawan masu rike da mukamai a zangon da ya gabata don su ci gaba da jan ragamar wannan aiki.
Babbar fatar da ake yi ita ce, Allah ya ba su karfin guiwar gudanar da wannan aiki don cimma nasarorin da ake bukata wajen hada kan Malaman Afrika da karfafa dankon zumunci a tsakanin su don su jagoranci al’umma zuwa ga sawaba da yardar Allah madaukakin Sarki. Kuma a gare shi muka dogara.
Allah ya yi dadin tsira da aminci ga Annabinmu Muhammad da iyalansa da sahabbansa.
Ku kalli wasu daga ciki hotunan wannan taro:
Laisser un commentaire