Bayani na 25 Kwanan Wata : 24/7/1441 = 19/3/2020
Bayanin Haxaxxiyar Qungiyar Malaman Afrika Akan Cutar Corona
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halicci mutum, ya girmama shi, kuma ya fifita shi akan da yawa daga cikin abubuwan da ya halitta. Tsira da aminci su tabbata ga Annabin shiriya, Annabin rahama, Muhammad xan Abdullahi da Alayensa da Sahabbansa gaba xaya. Bayan haka :
Haqiqa duniya ta cika da tsoro da firgici a wannan xan lokaci saboda cutar Coronabirus, cutar da ta fantsama cikin duniya, gabas da yamma, kudu da arewa, duk da wasu qasashen sun fi wasu cutuwa. Qasashenmu na kudancin sahara su ma basu tsira daga wannan masifa ba,duk da cewa waxanda suka kamu da wannan cuta a cikinsu ‘yan kaxan ne basu da yawa.
Wannan yanayi mai haxari da ake ciki, ya wajabtawa qasashe da garuruwa su xau matakin tunkarar wannan cutar da munanan abubuwan da take haifarwa. Don haka haxaxxiyar qungiyar malaman africa take fuskantar da waxannan jawabai zuwa ga hukumomi da jama’arsu a cikin waxannan qasashe da garuruwa :
1. Abu na farko : Qarfafa imani da yaqini akan ikon Allah Maxaukakin Sarki da tabbatar raunin xan adam. sabodawannan annoba da cututtuka da abubuwan da suke haifarwa dukkaninsu halittar Allah ne Maxaukakin Sarki, yana hore su, ya sake su yadda ya ga dama a bisa iliminsa da hikimarsa.
2. Kira zuwa ga hukomomi da su kyautata haxa kai da jagororin addini a qasashensu don haxa qarfi wajen tunkarar haxarin wannan annoba.
3. Kira zuwa ga malamai da masu wa’azi da limaman masallatai akan su bada himma wajen wayar da kan mutane akan bin tsare-tsaren da aka samar don fuskantar wannan annoba, ta hanyar amfani da abubuwan da masana a wannan fanni suka faxa, da abin da dalilai na shari’a suka nuna.
4. Idan xaukan matakai don tsayar da haxarin wannan annoba ya kai zuwa ga mahukunta sun yi umarni a rufe masallatai, to mu sani dalilai na shari’a sun nuna hallacin yin hakan, don kawar da cuta, kuma wajibi ne akan musulmi su bada haxin kai ga vangarorin da abin ya shafa don kyakkyawan zartarwa, sannan a umarci mutane su riqa yin salloli a gidajensu, har sai an samu canjin yanayi.
5. Kira zuwa ga tuba ga Allah mai girma da buwaya, da yawaita neman gafara, saboda tasirin haka wajen kawar da masifu.
6. Yawaita addu’a da qanqan da kai ga Allah Maxaukakin Sarki, musamman ma a lokutan da ake amsa addu’a.
Allah Maxaukakin Sarki muke roqo ya yaye mana wannan annoba, ya kiyaye mu da ikonsa da qarfinsa daga wannan cuta. Haqiqa Allah mai ji ne mai amsa addu’a. Tsira da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammad da Alayensa da Sahabbansa.
Dr. Said Burhani Abdoullah Dr. Seydou Madibaba Sylla
Laisser un commentaire