Bayani Mai Lamba: 30 Kwanan Wata: 05/02/1445 daidai da 22/8/2023
Wannan bayani ne da Majalisar Malaman Afurka ta fitar dangane da matsalar da take faruwa a qasar Nijar bayan juyin mulkin da Sojiji suka yi a qasar.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Maxaukakin Sarki. Tsira da aminci su tabbata ga amintaccen Manzonsa, wanda ya aiko domin rahama ga mutane, da Alayensa da Sahabbansa gaba xaya.
Bayan haka. Wannan Qungiya ta Malaman Afurka ta bibiyi abubuwan da suke faruwa a qasar Nijar sakamakon juyin mulkin da Sojoji suka yi wa Shugaban qasar, wato Muhammad Bazum. Al’amari wanda a sakamakonsa Haxaxxiyar Qungiyar Qasashe Renon Ingilishi, da suke yammacin afurka wato ECOWAS, da suke da manufofin tattalin arziki iri xaya, suka haxu suka zartar da hukuncin qaqaba wa qasar Nijar tsauraran takunkumma, suka kuma yanke hukuncin wajabcin shiga qasar da qarfin Soja domin mayar da Shugaba Bazum a kan karagar mulkinsa, idan har ba a iya cim ma hakan a cikin difulomasiyya da rowan sanyi ba. Haka kuma Qungiyar ta kalli matsayin daban-daban, wasu qasashe suka xauka a kan wannan al’amari.
To, saboda munanan sakamakon da waxannan matakai ka iya haifarwa ga qasar ta Nijar da sauran qasashen da suke wannan nahiyya, waxanda suka daxe da faxawa cikin matsalolon tavarvarewar sha’anin tsaro da na tattalin arziki; wannan Qungiya ta Malaman Afurka, da take da manbobi daga qasashe 47 da suke wannan nahiyya ta kudancin saharar Afurka ta fitar da wannan bayani bayan ta yi qwaqqwaran nazari kuma mai zurfi a kan wannan yanayi bisa ma’aunin manufofin Qungiyar da saqon da take xauke da shi zuwa ga duniyar Musulunci cewa tana kira ga duniya:
1. Qungiyar tana jajanta wa al’umar wannan qasa ta Nijar bias wannan mummunan yanayi da suka sami kansu a ciki. Suna kuma kiransu zuwa ga haquri da bar wa Allah komai, tare da watsar da duk wasu banbace-banbance da suke tsakaninsu domin ganin sun tsallake wannan siraxi cikin nasara
2. Qungiyar kuma tana kira ga xaukacin waxanda suke riqe da madahun iko a faxin duniya, da a yi duk qoqarin da ake iya yi domin sasantawa tsakanin Majalisar Sojijin Nijar da suke riqe da ragwamar mulkin qasar da Qungiyar qasashen Afurika ta ECOWAS domin ganin an janye wa qasar takunkunman da aka qaqaba mata ba tare da wani vata lokaci ba, an kuma kuvutar da ita daga faxawa bala’o’an yaqi, wanda ka iya haifar da miyagun matsalolin tsaro tare da qara dagule al’amurra a wannan nahiyya bayan sun riga sun tavarvare iyakar zarafi sakamakon ayyukan ta’addanci da wasu qungiyoyi suka mayar da hankalin a kansu a wannan yanki.
3. Haka kuma Qungiyar tana goyon baya tare da qarfafa qoqarin da waxansu Malamai daga qasar Najeriya da take maqwabtaka da Nijar xin suka yi na shiga tsakani. Qungiyar tana miqa cikakkar godiya da jinjina ga waxanda suka shirya al’amarin da duk waxanda suka taimaka ko suke da niyyar taimakawa a cikin ganin an walwale wannan matsala cikin rowan sanyi.
4. Qungiyar kuma tana jan hankali tare da faxakar da duniya a kan mummunan sakamakon da irin wannan kutse da qasashen qetare kan yi a wannan nahiyya kan haifar, wanda a qarshe yakan mayar da waxannan qasashe wani fage na gwabza yaqin biyan muradun kai, wanda a qarshe kuma al’umomin qasashen ne kan zama sha wuya ba su ji ba su gani ba.
5. A qarshe kuma wannan Qungiya na kira ga gaba xayan Musulmin naiyyar Afirka da, na cikin gida da waxanda suke zaune a waxansu qasashen duniya, su cigaba da yi wa mutanen qasar Nijar addu’a da roqon Allah ya nuna musu qarshen wannan jarabawa a cikin xan qanqanin lokaci ba tare da wata hasara ba.
Wa sallallahu alá Nabiyyiná Muhammadin wa alá Álihí wa Sahbihí taslíman kasiírá
Dr. Said Burhani Abdoullah Dr. Seydou Madibaba Sylla
Shugaba Babban Sakatare
Laisser un commentaire