Ecrit par & déposé en vertu de غير مصنف.

  • Majaisar Malaman Afrika
  • Kwamitin Fatawa da Luraswa.
  • Juma’a 1/06/1445 – 15/12/2923
  • Fatawa Mai Lamba: 17 – 45 a kan Hukuncin Tarayya da Waxanda ba Musulmi ba a Cikin Bukuiuwansu na Addini ko Taya su Murna

 

  1. Shimfixa:

Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai. Tsira da aminci su tabbata ga Shugaban halitta mai tsaira da aminci, da alayensa da sahabbansa wa sallama, tasliman kasira. Bayan haka:

Kafin bayyana wannan fatawa akwai waxansu tabbatattun abubuwa da hukunce-hukunce, ya zama wajibi mu yi nuni zuwa gare su, saboda kasancewarsu tushen da muka gina wannan fatawa a kai, day a zama wajibi a kan kowane Musulmi, ya yi imani ya kuma yi aiki, da su. Waxannan abubuwa da hukunce-hukunce  kuma su ne:

  • Babu wani addini ingantacce kuma karvavve a wurin Allah Maxaukakin Sarki, sai Musulunci: tabbacin haka kuwa shi ne faxar Buwayayyen Sarkin cewa: “Haqiqa addini a wurin Allah shi ne Musulunci.” (Ali Imran:19) “Duk wanda ya bi wani addini wanda ba Musulunci ba, Allah ba zai karvi ibadarsa ba. A ranar Lahira kuma zai tashi tare da hasararru.” (Ali Imran:85).

  • Haramun ne ga kowane Musulmi ya aikata wata ibada daga cikin ibadojin waxanda ba Musulmi ba, da a cikin addininsu kawai aka san su, ko tarayya da su a cikinsu, ta hanyar tafita inda ake yin ibadar, ko taimaka musu da wani abu, ko wani abu mai kama da wannan.

  • Haka kuma haramun ne ga duk wanda yake Musulmi, ya nuna soyayya da qauna, ko jivintar al’amarin duk wanda ba Musulmi irinsa ba. Musamman, a cikin al’amurran da suka shafi addini da ibadojinsu.

  • Kira da wa’azi zuwa ga Musulunci yana daga cikin abubuwan da suka wajaba a kan kowane Musulmi; tare da dagewa a kan haka a cikin hikima da basira da fasaha kamar yadda Allah Maxaukakin Sarki ya umurci Annabinsa Muhammaduce sallallahu alaihi wa sallam da gaya wa duniya cewa: “Ka gaya musu cewa: Wanna ita ce hanyata; ina kira zuwa ga Allah, ni da waxanda su ka bi ni.” (Yusuf:108). Wannan shi yake tabbatar da wajabcin nisantar duk wani abu da, yake iya kawo shakku da kokwanto da qyama tsakanin rukunin jama’ar da suke rayuwa a wuri xaya. Bisa wannan dalili ne, muka ga Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana ziyarar abokan zamansa waxanda ba Musulmi ba domin tabbatar da kyakkyawar mu’amala a tsakaninsu, da kuma rayawa da barin qofar da’awa buxe a tsakaninsa da su. Amma, tattare da haka babu inda tarihi ya nuna cewa, ya tava tarayya da su a cikin wasu ibadoji ko bukuwa nasu.

Waxannan bayanai da suka gabata, suna nunawa a fili cewa, tarayya da waxanda ba Musulmi ba a cikin wasu bukukuwa na ibadojinsu ko shiga Coci-cocinsu, abu ne day a haramta ga kowane Musulmi. Hujja a kan haka kuwa it ace faxar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam: “Duk wanda ya yi kama da wasu mutane, ya zama xaya daga cikinsu.” (Sunanu Abi Dawud:3512 / Albani kuma ya inganta shi a cikin Sahihu Abi Dawud). Ba kuwa don komai al’amarin ya zama haka ba, sai domin ksancewar bukukuwan shekara-shekara xin nan, suna daga cikin rukunai kuma ginshiqan addininsu, waxanda duniya ta san su, da su. Saboda haka muna qara nanatawa cewa, tabba! Haramun ne yin tarayya da su a cikin irin waxannan bukukuwa nasu, na shekara-shekara. Idan zancen buki ne ai, muna da manu bukukuwa na addini kamar yadda suke da su. Muna kuma da namu addini kamar yadda suke da nasu. To, kowa ya tsaya ga nashi.

  1. Hukuncin Taya Kiristoci Murnar Kirsimati:

Sakamakon zama a farfajiyar Afrika ta kudancin Sahara tare da maqwabtaka da waxanda ba Musulmi ba. Musamman, a wuraren da Musulmin su ne mafi qarancin adadi, za ka taras da cewa:

  • Mafi yawa daga cikin zuri’o’in da suke irin waxannan yankuna, sun samu ne daga zuria wadda ba Musulma ba. A haka kuma alaqa da zumunci, za su cigaba da kasancewa a tsakaninsu tattare da zaman addininsu ba xaya ba.

  • Sai ka taras cewa, waxanda ba Musulmin ba, sukan halarci wasu taruka da bukukuwa al’ada da ibada na Musulmi kamar bukun aure da walimar dawowar wasu daga aikin Hajji, da waxansu bukukuwan na daban. Sukan kuma je wa ‘yan’uwan nasu Musulmi, murna ko jaje ko tanzanko, idan an rasa wani masoyi ko wata musiba ta sauka.

  • Sukan kuma taya Musulmi murna a ranakun Idi ta hanyar gaya musu cewa: ‘Barkarku da sallah’ da makamancin haka.

  • Haka kuma a kodayaushe suna yi wa juna kyautar abinci sakamakon maqwabtaka da take tsakaninsu; ba sai lokacin wani buki ba. Musulmin kuma sukan aika wa ‘yan’uwan nasu kafirai naman layya a lokutan babbar Sallah.

To, a irin wannan yanayi da, tsakanin Musulmi da waxanda ba Musulmi ba, ake samun maqwabtaka da zumunci da wasu alaqoqi na daban da, rayuwar yau da kullum take wajabtawa, kamar aiki a Ma’aikata xaya ko abota a Makaranta, ko inda Malamin dab a Musulmi ba take duba aikin wani xalibi Musulmi, ko akasin haka. Ko likitoci da suke kula da marasa lafiya Musulmi, alhali su ba Musulmi ba. To, Musulunci ya samar da hukunci uku a irin waxannan yanaye-yanaye, kamar haka:

  • Duk abin da yake da alaqa da aqidah a irin wannan yanayi kamar bukin Kirsimati ko na faskhu ko na gina Coci, bay a halasta ga Musulmi ya yi tarayya da su ko ya taya su murna a ciki, domin gaba xayan waxannan al’amurra sun sava wa ginshiqan aqidar Musulunci.

  • Amma, abin da ake xauka cewa mayar da buki ne kawai. Sun yi mana saboda haka ya kamata mu ma mu yi musu. Musulunci yana kallon irin wannan da fuska biyu:

  • Na xaya shi ne:

Idan waxanda ba Musulmin ne ba, suka fara taya Musulmi murna a lokutan bukin Idinsu, ta hanyar gaya musu cew: ‘Barkarku da sallah’ ko ‘Allah shi maimaita mana.’ A irin wannan hali ya halasta ga Musulmi idan su, nasu Idin ya zo, su mayar musu da hannun baiwa tunda su ne suka fara gaishe mu. Gaisuwa kuwa, Allah Maxaukakin Sarki cewa ya yi game da ita: “Idan an gaishe ku da wata gaisuwa, to ku mayar da irinta ko wadda ta fi ta kyau. Haqiqa Allah, a kan dukan komai mai kiyayewa ne.” (Nisa’i:86). A farkon Musulunci, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kasance, idan wanda ba Musulmi ba ya gaishe shi, sai yakan mayar masa da cewa: ‘Assamu alaika’ ko ‘wa alaika.’  Sai Allah Maxaukakin Sarki ya gaya masa cewa: “Ai, Allah bai hana ku kyakkyawar mu’amala da waxanda bas u yaqe ku ba a cikin addini, bas u kuma fitar da ku daga gidajenku ba; ku kyautata musu ku kuma yi musu adalci. Lalle ne Allah yana son masu adalci.” (Almumtahana:8).

Amma fa a lura! Hakan tana halasta ne idan su ne suka fara taya Musulmi murna xin. Ko a hakan ma, damar da Musulunci ya bayar ta mayar musu da hannun baiwa xin, tana da hukunci biyu kamar haka:

  • Baya halasta Musulmi ya taya su murna shi ma, sai idan yana da yaqinin cewa haka, zai iya zama dalilin shiriyar wanda ya taya murna xin zuwa ga Musulunci. Ko kuma zai sa a samu cikakken zaman lafiya a tsakaninsa da Musulmi; ba cuta ba cutarwa. Musamman, a lokacin da ake tabbacin cewa kowane lokaci ana iya samun varkewar rikici tsakanin Musulmi da waxanda ba Musulmi ba a yankin. To, babu laifi a taya su murna a kuma yi musu addu’a da fatar shiriya zuwa da Musulunci, ko a asirce. A karatu, wannan matsayi ne shi ake kira ‘rinjayar da alhairi’ wato tarjihul- maslahah.

  • Amma, idan taya su murna xin zai sa su qara xaga karan hanci tare da jin cewa Musulmi sun qasqanta har sun miqa wuya domin ga shi suna taya su murna. A irin wannan yanayi bas hi halasta, ko alama! Domin wajibi ne Musulmi da Musulunci su zama su ne sama har abada; babu wani abu a kansu.

  • Na biyu shi ne:

Taya su murna yana halasta idan al’amarin da ake kai, abu ne da ake kallo a matsayin al’ada, kamar bukin buxe sabon gida ko dawowar matafiyi ko samun wani babban matsayi. To, babu laifi idan Musulmi ya taya wanda ba Musulmi ba, murna a ciki. Musamman, idan akwai kyakkyawar alaqa da fahimtar juna a tsakaninsu, ko abota ko maqwabtaka ko wata alaqa irin ta zaman yau da kullum, irin wadda take wajabta zaman lumana da amana da aminci, irin waxanda shari’ar Musulunci da kyakkyawar al’ada suka yarda da su. Babu laifi a irin wannan tunda Allah Maxaukakin Sarki ya bayyana yadda ya kamata zamantakewa ta zama tsakanin Musulmi da wanda ba Musulmi ba a cikin Littafinsa mai tsarki, kamar yadda aka bayyana a baya kaxan, da cewa: “Ai, Allah bai hana ku kyakkyawar mu’amala da waxanda bas u yaqe ku ba a cikin addini, bas u kuma fitar da ku daga gidajenku ba; ku kyautata musu ku kuma yi musu adalci. Lalle ne Allah yana son masu adalci.” (Almumtahana:8).

 

Duk kyakkyawar mu’amalar da Musulmi zai yi da wanda ba Musulmi ba a wannan babi, sunanta ‘kyakkyawar xabi’a’ irin wadda Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya umurci Abuzarrin raliyallahu anhu, da ita da cewa: “Ka ji tsoron Allah duk inda kake. Ka kuma biyar da kyakkyawan aiki a kan mummuna, sai ya shafe zunubin. Sa’annan ka yi mu’amala da mutane da kykkyawar xabi’a. (Tirmizi:4/355). Abu Isah ya ce: ‘Wannan Hadisi ne ingantacce. A lura da kyau kuma, cewa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya yi: Sa’annan ka yi mu’amala da mutane…..”  bai ce: Sa’annan ka yi mu’amala da musulmi ba…..”  Wannan kuwa, ko ba a gaya maka ba, ka san wani launi ne na da’awah zuwa ga Allah Maxaukakin Sarki, ta hanyar hikima da kyakkyawan wa’azi a zuci da baki da aikace.

 

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ya zama wajibi a kan kowane Musulmi ya yi kaffa-kaffa a lokacin da yake taya su murna xin a kan waxansu al’amurra na al’ada, kada ya furta wata kalma da za ta mayar da su kamar Musulmi a wurinsa, ko ta nuna amincewarsa da abin da suke a kai. A misali yana iya gaya musu cewa: “Allah shi kama maku,” yana nufin wai: “Allah ya shirya su.” Ko ya gaya musu cewa: “Allah ya maimaita da alhairi da shiriya.” Ko waxansu kalmomi masu kama da waxannan, da suke xauke da addu’a da roqon Allah shiriya zuwa gare su, daga vatan da suke ciki, ba kuma tare da yarda da nuna wata yarda da aqidarsu ko zaman addininsu gaskiya ba. Musulmi zai miqa wuya ne ga irin wannan tsari kawai, saboda zamansa wata hanya ta faxaxa da’awah da xaure zumuncin da yake tsakaninsa da waxannan mutane, da kuma kyakkyawar mu’amala, waxanda dukansu, abubuwa ne da shari’ar Musulunci take kira zuwa gare su a alqur’ani da Sunnah, domin tabbatar da darajar xan Adamu.

 

Allah shi ne Masani. Wa sallallahu ala Sayyidina Muhammadin wa alah Álihi wa Sahbihi wa sallam.

 

III. Manbobin Kwamitin Fatawa da Shiryarwa a Majalisar Malaman Afrika:

Fadhilatu As-Shekh Al’ustaz Dr. Muhammad Ahmad Lauhu, Senigal        Shugaba.

Fadhilatu As-Shekh Al’ustaz Dr. Jelani Hidhir, Ethiopia                             Muqarran

Fadhilatu As-Shekh Al’ustaz Dr. Hassan Muhammad Buwá, Uganda        Memba

Fadhilatu As-Shekh Al’ustaz Dr. Abubakar Bah, Senigal                            Memba

Fadhilatu As-Shekh Al’ustaz Dr.Siyaka dabara, Kod-Debuwa                    Memba

Fadhilatu As-Shekh Al’ustaz Dr.Muhammad Tarawi, Mali                          Memba

Fadhilatu As-Shekh Al’ustaz Dr.Abdurraz Husain, Jibuti                            Memba

Fadhilatu As-Shekh Al’ustaz Abubakar Muri. Laberiya                               Memba

As- Sayyidah Al’ustazah Mamu Jariyah Nayaniga, Senigal                         Memba

 

 

Sanarwa Daga:

Ustazu- Dr, Muhammad Ahmad Lauhu

Shugaban Majalisar malaman Afrika

Shugaban Tsangayar  Afrika da Nazarin Addinin Musulunci, Senigal

 

 

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *