Bayanin Hadaddiyar Ƙungiyar Malaman Afirka game da Ziyarar da wasu Limamai da Masu Wa’azi daga Afirka suka kai wa Ƙasar Yahudawan Sihiyoniya Mai Mamaya
______
Lambar Bayani: 32
Kwanan wata: 20/6/1447 AH = 12/12/2025 M
______
Dukkan Yabo da Godiya sun tabbata ga Allah Maɗaukaki, Wanda Ya ce: “Muminai maza da muminai mata masoya kuma mataimakan juna ne”. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Annabinmu Muhammad wanda ya ce: “Mumini ga mumini kamar jiki guda ɗaya ne”, da iyalan gidansa, sahabbansa, da waɗanda suka bi su da kyautatawa har zuwa Ranar Alƙiyama.
Bayan haka:
Duba da nauyin da ya rataya a wuyan Hadaddiyar Ƙungiyar Malaman Afirka na addini, da na kula da tarbiyyar mutane da inganta rayuwar su, haka nan don sauke nauyin wajabcin nasiha da yi wa juna wasiyya da gaskiya, kuma don tabbatar da goyon bayan Masallacin Al-Aqsa (wato Masallacin Kudus), da kuma taimaka wa gwagwarmayar ’yan’uwanmu ‘Yan Falasdinu a kan zaluncin mamaya da suke fama da shi. Duba da wadannan dalilai Hadaddiyar Ƙungiyar take fitar da wannan Bayani game da al’amarin ziyarar da wasu limamai da malaman addinin Musulunci daga Afirka suke kaiwa bangaren kasar Falasdinu da aka mamaye, cikin wasu tafiye-tafiye da mahukuntan mamayar suka shirya kuma suka ɗauki nauyinsu, da hujjar wai nuna musu halin da ake ciki a kasar da kuma kai su yawon buɗe ido na musamman, wanda farfagandar Isra’ila ke bayyana kanta a matsayin mai nuna ’yan’uwantaka da jituwa tsakanin addinai.
Hadaddiyar
Ƙungiyar tana bayyana cikakken ƙin amincewa da yin Allah-wadai da shigar wasu limamai da malaman addinin Musulunci daga wasu ƙasashen Afirka cikin irin waɗannan ziyarce-ziyarce masu cike da shakku, sannan tana mai fayyace matsayinta a cikin sakonni masu zuwa:
1. Ya tabbata ga Ƙungiyar cewa wasu limamai da malaman addinin Musulunci sun kai wannan ziyara bisa gayyatar hukumomin Isra’ila.
2. Ziyarar shugabanni da manyan malamai zuwa ƙasar Falasdinu da aka mamaye a irin wannan yanayin da wannan lokaci, da kuma ta wannan hanyar gayyata, babban kuskure ne kuma faɗuwa ƙasa ne mai tsanani, wanda ke buƙatar bayani da neman afuwar al’ummar Musulmi, domin hakan ya saɓa wa ijma’in malaman al’umma da kuma ra’ayin yawancin Musulmi. Waɗanda suka shiga irin waɗannan ziyarce-ziyarce ba sa wakiltar matsayar al’ummomin Musulmi na Afirka game da ’yan’uwansu a Falasdinu da ke cikin halin mamaya!
3. Waɗannan ziyarce-ziyarce suna nuna ba wa mahukuntan mamaya na Isra’ila halaccin da ba su da shi.
4. Ƙungiyar tana ganin cewa irin wannan ziyara zuwa ga ƙasar mamaya na iya shiga cikin nau’o’in daidaitawa da ƙasar mamaya (normalization), wanda hakan ke ƙarfafa mamayan ya ci gaba da munanan ayyukansa da laifukansa kan al’ummar da basu ji ba basu gani ba, da ’yan’uwanmu a Falasdinu da ake mamaya.
5. Ƙungiyar tana kira da a amince da haƙƙin yin kowace irin gwagwarmayar kwatar ‘yanci domin kawar da mamaya daga dukkanin kasarFalasdinu gaba ɗaya, musamman Masallacin Al-Aqsa.
6. Ƙungiyar tana kira ga dukkan Musulmi da su ɗauki matakai domin hana maimaituwar irin waɗannan ziyarce-ziyarce ta hanyar sauke nauyin wajabcin yin nasiha ga masu kai irin wannan ziyarar cikin kyakkyawar hanya.
7. Ƙungiyar tana yin Allah-wadai da matsayoyin ƙasashe da hukumomin da ke goyon bayan mamayar Falasdinu, wanda hakan ke ƙarfafa zalunci da aka daɗe ana yi wa mutanen Falasdinu tsawon shekaru da dama har zuwa yau, kuma wanda ya jawo rikice-rikice masu yawa a duniyarmu a yau.
8. Ƙungiyar za ta yi aiki domin fitar da Fatawa don bayyana hukuncin shari’a daga Kwamitin Fatawa na Ƙungiyar game da hukuncin ziyartar yankunan da ake mamaya bisa gayyatar hukumomin mamaya, da kuma hukuncin abubuwan da suke biyo bayan hakan.
9. A ƙarshe, Ƙungiyar tana ƙarfafa dukkan Musulmi da su yi addu’a ga malamansu, tare da roƙon Allah Ya ba su dacewa, gyara, da yin daidai a maganganunsu da kuma a shawarwarinsu.
Allah Ya yi salati da sallama masu yawa ga Annabinmu Muhammad, da iyalan gidansa da sahabbansa.
Dr. Said Burhani Abdoullah Dr. Seydou Madibaba Sylla
Shugaba Babban Sakatare
Laisser un commentaire