Ecrit par & déposé en vertu de غير مصنف.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

BAYANIN HADADDIYAR KUNGIYAR MALAMAI TA AFRIKA A KAN HALIN DA AL’UMMAR MUSULMIN ROHANJIA NA YANKIN ARAKAN SUKE FUSKANTA NA KISAN KIYASHI

Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai. Tsira da aminci su kara tabbata ga mafi darajar Annabawa; Annabi Muhammad, da iyalansa da Sahabbansa baki daya. Bayan haka:

Tabbas, halin da al’ummar Musulmin Rohanjia na yankin Arakan suke fuskanta na kisan kiyashi yana da tsananin ta da hankali. Wannan ta’addanci kuwa gwamnatin Myanmar ce take yin sa ta hannun sojojinta wadanda akasarinsu masu bin addinin Budda ne. A dalilin ta’addancin kuma an rasa dubun dubatar rayukan Musulmi, an kuma mayar da wasu da ba su kirguwa a matsayin ‘yan gudun hijira da kuma wadanda aka kewaye. Ga kuma gidajensu da aka kokkona, da kadarorinsu masu dinbin yawa da aka halaka. Tare da haka duniya ta yi gum kamar ba ayi komai ba. Har da kasashen Musulmi ba su motsa ko karan dawa ba. Wannan lamari yana da muni matuka, kuma yana kara tabbatar da cewar da ake yi ana kariyar hakkin bil Adama zunzurutun karya ce kawai don cim ma wasu manufofi.

Bisa la’akari da cewa, Allah ya dora ma Malamai a matsayinsu na Magadan Annabawa su bayyana gaskiya a cikin kowane hali, kamar yadda madaukakin Sarki ya ce: “Ka ambata lokacin da muka riki alkawalin wadanda aka ba su littafi, cewa, lallai ne ku bayyana shi ga mutane, kuma kada ku boye shi..”. Da kuma cewar da Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallam ya yi a Hadisin da Muslim ya ruwaito daga Abu Huraira Radhiyallahu Anhu: “Musulmi dan uwan Musulmi ne; ba ya zaluntar sa, ba ya tozarta shi kuma ba ya wulakanta shi”. Bisa ga wannan, mu da muka sa hannu a wannan takarda a madadin Kungiyoyi da Majalisu daban daban muna ganin ya zama wajibi mu bayyana abubuwa kamar haka:

Na farko: Taimakon yan uwanmu Musulmi na yankin Arakan da hana zaluntar su da yi masu kisan babu gaira babu dalili da korar su daga gidajensu wajibi ne da Allah ya dora ma kowane mai iko. Daga cikin wadan da wannan wajibi ya hau kansu kuwa har da gwamnatocin kasashen Musulmi, ta dukkan hanyoyin da suke iyawa, kamar:

Yanke huldar diflomasiyya da ta kasuwanci da wannan azzalumar gwamnati, da tilasta ma hukumomin manyan kasashe su sa ma ta takunkumi da sauran tsauraran matakan da za su hana su ci gaba da zaluntar yan uwanmu na Arakan. Haka nan da ba da dama ga jami’ai da kungiyoyin kare hakkin dan Adam da yan jarida su shiga a wadannan yankunan don su bayyana ma duniya gaskiyar abin da ke faruwa. Da kuma ba da dama ga masu kai agaji don su taimaki masu sauran rai da wadanda suke a tantunan gudun Hijira da ke cikin Burma, daga nan kuma a sa ido ga dokokin kasar da manufar kwatanta su da dokokin da Majalisar dunkin duniya ta amince da su game da hakkin bil Adama.

A nan ya zama dole mu yaba ma kokarin da gwamnatin kasar Turkiyya ke yi ta fuskar diflomasiyya don rage radadin da yan uwan namu na Arakan suke ciki. Muna kuma amfani da wannan dama mu yi kira ga gwamnatocin kasashen Musulmi da su sani cewa, kyale wadancan bayin Allah a irin halin da suke ciki tare da rashin taimakon su yana iya janyo wasu ukubobi na Allah madaukakin Sarki tun a nan duniya kafin gobe kiyama.

Yana da kyau duniya ta sani cewa, duk wanda bai hana wannan zalunci ba yana ji yana gani alhali kuma yana da abin yi to, Allah zai hukunta shi kamar da shi aka yi. Haka ma duniya za ta dauke shi munafuki idan ya daga baki ya ce, ya san hakken dan Adam.

Na biyu: abin da ake bukata daga kungiyar hadin kan kasashen Musulmi (OIC) da majalisar hada kan duniyar Musulmi (IWL) da dukkan masu ruwa da tsaki a wannan sha’ani na kungiyoyin kare yancin dan Adam da sauran su shi ne su yi iyakar kokarinsu don taimaka ma wadannan bayin Allah da dauke zaluncin da ake yi daga kansu. Kuma su yayata maganarsu a ko ina.

Na uku: Muna kira ga dukkan kungiyoyi da masu ba da agaji da su tashi tsaye wajen sauke nauyin da yake kan su don sassafta wannan bala’i da yan uwanmu suka tsinci kansu a ciki ta hanyar ba da agajin gaggawa da hada kai da duk masu irin wannan kyakkyawar manufa don agaza masu. A nan muna ba da sanarwar cewa, tuni an ta da wani ayari ta

re da hadin guiwar kungiyar “Insan Vakfi” ta kasar Turkiyya don taimaka ma al’ummar Rohanjia.

Na Hudu: Muna kira ga limaman Masallatai da su yi Kunuti a cikin salloli biyar da aka saba suna masu kai kuka zuwa ga Allah don ya kuranye ma wadannan yan uwanmu wannan damuwa da suke cikin ta. Haka kuma su gabatar da hudubobi a jum’ah mai zuwa don sanar da jama’ar Musulmi halin da yan uwansu suke ciki.

Haka kuma, muna kara kira da babbar murya ga al’ummar Musulmi a ko ina su yi abinda suke iyawa na addu’a da taimako kowa gwargwadon ikonsa.

Haka ma yana da kyau a shirya jerin gwano a duk kasashen da tsarinsu yake ba da damar yin hakan, musamman don a isar da sakon fushin da al’ummar Musulmi take cike da shi ga jakadun kasar Burma kan jinainan yan uwanmu da ake zubarwa.

Na Biyar: Muna tunatar da yan uwanmu Musulmin Arakan cewa, nasara tana tare da hakuri, kuma sauki yana tare da tsanani, sannan kunci yana tare da sarari, kuma Allah mai kuranye damuwa ne ga bayinsa. “Hakika, Allah yana tare da wadanda suke taqawa, kuma wadanda suke su ne masu kyautatawa”.

Muna rokon Allah ya kuranye ma yan uwanmu na Burma halin kunci da suke ciki, ya daukar masu fansa a kan wadanda suke zaluntar su. Allah majibincin haka ne kuma mai ikon yi babu mai hana shi.

Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabinmu Muhammad da iyalansa da Sahabbansa baki daya.

Laisser un commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée. Les champs obligatoires sont indiqués avec *