BAYANIN HADADDIYAR KUNGIYAR MALAMAN AFRIKA GAME DA MATAKIN DA SHUGABAN AMURKA DONALD TRUMP YA DAUKA NA MAYAR DA OFISHIN JAKADANCINSU DA ISRA’ILA ZUWA BIRNIN QUDUS
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Manzon Allah da iyalansa da Sahabbansa baki daya. Bayan haka :
Allah Tabaraka wa Ta’ala yana cewa : « Tsarki ya tabbatar ma Allah wanda ya yi tafiyar dare da bawansa daga Masallaci mai alfarma zuwa Masallaci mafi nisa wanda muka sanya albarka ga sassansa » Suratul Isra’i : 1
Bisa ga manufar hadaddiyar kungiyar Malaman Afrika ta kulawa da al’amurran Musulmi na duniya, muna sanar da duniya cewa, mun yi allawaddai da wannan matakin da shugaban Amurka ya dauka na mayar da ofishin jakadancin Amurka a Isra’ila zuwa birnin Qudus ta Gabas wadda Yahudawa suka mamaye. Babu shakka wannan mataki fito na fito ne karara da ababe masu alfarma na Musulmi, abin da zai bakanta ran Musulmi sama da miliyan dubu da dari biyar da suke a cikin fadin duniya. Wannan kungiya tana kara ba da tabbacin cewa, wannan mataki al’ummar Musulmi ba za ta karbe shi ba. Kuma wajibi ne a kan mu mu bayyana ma duniya rashin amincewarmu.
Wannan hadaddiyar kungiya tana kira ga al’ummar Falasdinawa da dukkan kungiyoyinta da jama’arta su fito karara don tunkarar wannan danyen aiki. Dole ne su ci gaba da yaki da wannan mummunar siyasa ta ci gaba da mamayar yankunansu da ake yi. Kamar yadda wannan kungiya take ba su tabbacin goyon bayan al’ummar Musulmin Afrika ga baki daya ga jihadin Falasdinawa na kwatar yancinsu da dawo da yankunansu. Haka kuma muna neman duk Musulmi a inda suke su fito su bayyana damuwarsu da fushinsu a kan wannan shaidanin mataki da Amurka ta dauka don taimakon mutanen Qudus da Falasdinawa baki daya. Dole ne a samar ma al’ummar Falasdinawa yanci a kori Yahudawa yan kama wuri zauna.
Wannan kungiya tana kira da babbar murya ga shugabannin kasashen larabawa da na sauran kasashen Musulmi da su hada kai wuri daya don tunkarar wannan shaidaniyar shawara da Amurka ta yanke da dukkan hanyoyin da suke da iko wadanda doka ta amince. Kamar yadda muke kira ga mahukuntan kasashen larabawa su hada karfi da karfe don kariyar birnin Qudus mai albarka da yin watsi da duk wata yarjejeniya wadda za ta sa a mika wannan birni ga makiya, ko ma duk wani yanki na kasar Falasdinu.
Haka kuma wannan kungiya tana rokon ma’aikatun lamurran addini a kasashen larabawa da na Musulmi su yi amfani da Masallatai da wuraren wa’azi don yi ma al’umma bayanin halin da Masallacin Qudus da Falasdinawa suke ciki, da kuma bayanin matsayinsu da martabarsu a Musulunci tare da bayyana hatsarin barin Yahudawa yan kama wuri zauna su ci karensu babu babbaka a wannan wuri mai albarka. Allah Tabaraka wa Ta’ala ya ce : « Ya ku wadanda suka yi imani ! Ku yi hakuri kuma ku yi hakurceceniya, kuma ku yi ribadi, kuma ku ji tsoron Allah ko da za ku samu rabauta ». kuma ya ce : « Hakika, mu wallahi muna taimakon manzanninmu da wadanda suka yi imani a cikin rayuwar duniya da kuma ranar da shaidu za su tsayu ».
Tsira da aminci su kara tabbata ga shugabanmu Muhammad da iyalansa da Sahabbansa baki daya.
Shugaban Kungiya Babban Sakatare
Dr. Saïd Bourhani Abdallah Dr. Seydoud Madibaba Sylla
Laisser un commentaire