HAXAXXIYAR QUNGIYAR MALAMAI TA AFRIKA
Bayani na 24 30 – R/Awwal/ 1441 A.H 28/11/2019
A Daina Kiran ‘Yan Ta’adda Da Sunan “Mujahidai”
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da aminci su tabbata ga Annabin shiriya da rahama, Annabi Muhammad xan Abdullahi da iyalansa da sahabbansa baki xaya.
Bayan haka, Haxaxxiyar qungiyar Malamai ta Afrika ta lura da yadda wasu kafafen yaxa labarai da wasu mutane – cikin su har da mahukunta – suke kiran ‘yan ta’adda masu xaukar makami suna kashe al’umma babu gaira babu dalili, suna kiran su da sunan “Mujahidai”.
Waxannan qungiyoyin sun watsu sosai – kamar yadda muka sani – a sassa daban daban na Afrika. Kuma wannan abin takaici ne matuqa.
Don haka wannan qungiya mai suna a sama tana kira da babbar murya a kan a daina amfani da wannan suna mai daraja na mutanen kirki akan waxanda suke ta’addanci da firgita bayin Allah, tare da watsa varna a bayan qasa. Wannan kira kuwa ya shafi kowa da kowa, musamman ‘yan jarida da mahukunta da masu amfani da kafofin sada zumunta da sauran jama’a. Muna son masu amfani da wannan sunan a kan ‘yan ta’adda su yi la’akari da abubuwa kamar haka:
-
Kiran waxancan mutane da sunan “Mujahidai” munanawa ce babba ga addinin Musulunci, sun sani ko basu sani ba, domin Jihadi wani muhimmin abu ne, kuma yardajjen aiki ne mai matsayi da daraja a addinin Musulunci, wanda an san tarihinsa da darajarsa da dokokinsa a addinin musulunci, babu inda ya haxu da ayyukan ta’addancin da waxancan mutane suke yi.
-
Kiran waxancan mutane da sunan “Mujahidai” qarfafawa ne da taimako a gare su a fakaice.
-
Kiran waxancan mutanen da sunan Mujahidai zai iya jan da yawa daga cikin mutane zuwa ga shiga cikinsu, ko taimakonsu, ko tausaya masu, ko sha’awar yin aiki irin nasu, wanda hakan taimakawa abin da suke yi ne na ta’addanci.
Daga qarshe, wannan qungiya tana neman al’umma su haxa kai gaba xaya don kawo qarshen fitinu, da tashe tashen hankula, tare da dawo da aminci da zaman lafiya a qasashenmu.
Dr. Said Burhani Abdoullah Dr. Seydou Madibaba Sylla
Shugaba Babban Sakatare
Laisser un commentaire