Bayani Mai Lamba: 31
Kwanan Wata: 26/03/1445 daidai da 12/10/2023
Wannan bayani ne da Majalisar Malaman Afurka ta fitar dangane da matsalar da take faruwa a qasar Falasxinu da ake yi wa take da Larabci Xúfánul- aqsá.
Godiya ta tabbata ga Sarkin nan da ya yi isrái da bawansa a cikin dare, daga Masallacin Makka zuwa Masallacin Qudus. Tisra da amincin Allah su tabbata ga Annabinsa Muhammadu xan Adbullahi sallallahu alaihi wa sallah, wanda ya ba wa waccan dabba mai suna Buráqa, da aka yi waccan tafiya da ita, da Alayensa da Sahabbansa, da waxanda suka bi tafarkinsu har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka. Bias la’akari da irin girman da Masallacin Qudus yake da shi a wurin al’umar Musulmi, Majalisar ta bibiyi abubuwan da suka faru a wannan yanki, da zimmr goya wa Musulmin Falasxinu baya a kana wavvasar da dakarunta suka na bajinta, ta hanyar kai hare-hare ga Isra’ilawa ‘yan kama wuri zauna, wanda suka kira Xúfánul- aqsá; da cewa wannan aiki nasu halastacce ne a idon doka. Shi kuma martanin das u ‘yan kama wuri zauna suka yi, majalisar ta kale shi a matsayin zalunci irin wanda suka saba yi a kan mazauna birnin Zirin Gáza.
Bisa wannan ne, tare da la’akari da manufofin wannan Majalisa ta fitar da waxannan bayanai, dangane da waxannan abubuwa da suke faruwa, kamar haka:
1) Wnnan Majalisa tana goyon bayan wannan gwagwarmaya da Falasxinawa ke a kowane mataki da kowane matsayi, domin ganin an kawo qarshe mamayar da Isra’ilawa suke yi wa mazaunan Falasxinawa da Masallacin Qudus, musamman.
2) Wannan Majalisa tana kira ga xaukacin duk wanda yake son adalci da tabbatarsa a bayan qasa, duk inda yake a faxin dunya; zuwa ga goya wa Falasxinawa baya, fararen hula daga cikinsu da waxanda suke xauke da makami. A taimaka musu ta kowace hanya domin tabbatar da samun haqqoqansu da ‘yanto masallacin Qudus daga hannun Yahydawa ‘yan kama wuri zauna.
3) Haka kuma majalisar tana Allah waddai da qasashe da hukumomin da suke goyon bayan mamayar da ake yi wa Falasxinawa, tare da bayyana hakan a matsayin tsabar zalunci, wanda aka xauki tsawon shekaru ana yi wa Falasxinawa.
4) Majalisar kuma tana kira tare da tabbatar wa duniyar Musulunci da, wajabcin qarfafawa da yawaita bayanai da wayar da kan al’umma a cikin kafafen watsa labarai da saurarn hanyoyin sadarwa na zamani, da kuma a cikin manhajojin karantarwa a matakai daban-daban.
5) A qarshe kuma Majalisar na kira ga al’umar Musulmi a kan a yawaita addu’o’i da alqunuti da roqon Allah Maxaukakin Sarki ya taimaki waxannan ‘yan’uwa namu da ke falasxinu dangane da qasqancin da suke fuskanta a hannun Yahudawa ‘yan kama wuri zauna da sauran magoya bayansu. Muna roqon Allah Mazaukakin Sarki ya ba su nasara, ya taimake su, ya tabbatar da duga-dugansu. Wa sallallahu ala sayyidina Muhammadin wa ala alihi wa sahbihi wa sallam tasliman kasiran.
Dr. Seydou Madibaba Sylla Dr. Said Burhani Abdoullah
Babban Sakatare Shugaba
Laisser un commentaire